An Yankewa Wasu Yan Luwadi Hukuncin Kisa a Jahar Bauchi.


Wasu Yan luwadi kenan da aka yankewa hukuncin kisa a jahar Bauchi wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta yankewa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, bayan an same su da laifin yiwa wasu yara luwadi, a Ningi dake jihar Bauchi.


Kotun ta jihar Bauchi ta samu mutanen uku, da suka hada da matasa biyu da kuma wani babban mutum da ya kai sama da shekara 70 da haihuwa, da wannan laifi, wanda suka amsa.


Sai dai wani jami’in kotun wand ya yi wa BBC bayani ya ce babu wani lauya da ya wakilci mutanen uku a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.